24 Yuli 2017 - 18:37
 An Kame Wasu Mutane Da A Ke Zargin 'Yan Ta'adda Ne A Mali

Majiyoyin tsaro a kasar Mali sun sanar da cafke wasu mutane da ake zargin cewa suna da alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda a arewacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayar da rahoto daga birnin Bamako cewa, jami'an tsaron kasar Mali tare da hadin gwiwa da jami'an sojin kasar Faransa sun kai samame a wani wuri a kusa da birnin Gao, inda suka kame wasu mutane tare da tarin makamai masu yawa.

Wannan dai yana daya cikin ayyukan hadin gwiwa da bangarorin biyu suka gudanar a cikin nasara, a yunkurinsu na murkushe 'yan ta'adda da suke yin barazana ga harkar tsaron kasar.